Haramtacciyar Kasar Isra'ila Ta Fice Daga Hukumar "Unesco"
Babbar sakatariyar kungiyar ta "Unesco' Audrey Azoulay ce ta sanar da fitewa haramtacciyar kasar ta yahudawa daga kungiyar ta kasa da kasa a jiya juma'a.
Tun a ranar 12 ga watan Oktoba na shekara mai karewa ne pira ministan haramtacciyar kasar Isra'ila Benjamin Netanyahu ya sanar da kuduri ficewa daga kungiyar ta ilimi da al'adu ta Majalisar Dinkin Duniya.
Ita ma kasar Amurka ta sanar da aniyarta na ficewa daga cikin kungiyar ta "Unesco" saboda abinda ta kira kiyayyar da kungiyar take nunawa haramtacciyar Kasar Isra'ila. A ranar 31 ga watan Decemba ne dai Amurkan za ta fice daga cikin kungiyar.
Natenyahu ya bayyana matakin Amurkan na ficewa daga "Unesco;' da cewa jarunta ce.
Kungiyar ta fitar da kuduri ne a ranar 2 ga watan Mayu da a ciki ta zargi haramtacciyar Kasar Isra'ila da keta dokokin kasa da kasa dangane da birnin kudus.