Amurka Ta Yi Wa Gwamnatin Palasdinawa Barazanar Dakatar Da Taimakon Kudi
Jan 03, 2018 06:16 UTC
Shugaban kasar Amurka Donald Trump ne ya yi wa palasdinawan barazanar saboda sun ki amincewa da shirin mika wuya ga haramtacciyar kasar Isra'ila
Trump ya rubuta a shafinsa na Twitter cewa: "Ba kasar Pakistan ba ce kadai wacce take karbar biliyoyin daloli daga fadar White ba tare da wani abu ba, kasashe da wasu daidaikun mutane ma suna karba. Ga misali a kowace shekara Amurkan na bai wa Palasdinawa miliyoyin daloli, amma ba su yin godiya."
Bugu da kari Trump ya ce; Me zai sa Amurka ta ci gaba da bai wa Palsdinawa wadannan makudan kudaden.
Ita ma jakadiyar Amurka a Majalisar Dinkin Duniya Nikki Haley ta ce; matukar Palasdinawa ba su koma kan teburin tattaunawa ba to Amurka ta daina taimaka musu