Kungiyar Kasashen Musulmi Ta Yi Allawadai Da Harin Brussels
https://parstoday.ir/ha/news/world-i2812-kungiyar_kasashen_musulmi_ta_yi_allawadai_da_harin_brussels
Kungiyar kasashen musulmi ta yi Allawadai da harin da aka kai a birnin Brussels na kasar Belgium a jiya Talata, tare da bayyana hakan da cewa aiki ne na ta'addanci.
(last modified 2018-08-22T06:58:01+00:00 )
Mar 23, 2016 00:20 UTC
  • Kungiyar Kasashen Musulmi Ta Yi Allawadai Da Harin Brussels

Kungiyar kasashen musulmi ta yi Allawadai da harin da aka kai a birnin Brussels na kasar Belgium a jiya Talata, tare da bayyana hakan da cewa aiki ne na ta'addanci.

Babban sakataren kungiyar Iyad Amin Madani shi ne ya sanar da hakan, inda ya ce suna yin Allawadai da wannan aiki na ta'addanci, kamar yadda suke yin Allawadai da kowane irin aiki na ta'addanci a ko'ina nea cikin duniya, tare bayyana hakan da cewa ba shi a cikin koyarwar addinin muslunci.

Kungiyoyin musulmi a kasashen Birtaniya, Spain da sauran kasashen turai da dama, sun yi Allawadai da wannan hari, tare da nisa kansu da hakan, tare da bayyana cewa masu aikata hakan ba su wakiltar musulmin nahiyar turai.

Kungiyar ISIS mai dauke da akidar nan ta kafirta musulmi da ke da'awar jihadi, wadda ke samun dauki daga wasu gwamnatocin larabawa, ta sanar da cewa ita ce ke da alhakin kai wanann hari.