Sakatare Janar Na MDD Zai Ziyarci Kasar Kwango
https://parstoday.ir/ha/news/world-i28633-sakatare_janar_na_mdd_zai_ziyarci_kasar_kwango
Kakakin Sakatare-Janar na MDD ya sanar da amincewar shugaban jamhoriyar Demokaradiyar Kwango na ganawa da Sakatare janar na MDD da Shugaban Kwamitin Kungiyar Tarayar Afirka.
(last modified 2018-08-22T07:01:29+00:00 )
Feb 28, 2018 02:47 UTC
  • Sakatare Janar Na MDD Zai Ziyarci Kasar Kwango

Kakakin Sakatare-Janar na MDD ya sanar da amincewar shugaban jamhoriyar Demokaradiyar Kwango na ganawa da Sakatare janar na MDD da Shugaban Kwamitin Kungiyar Tarayar Afirka.

Kamfanin dillancin labaran kasar Faransa ya nakalto Stephane Dujarric mai magana da yawun sakatare janar na MDD na cewa Shugaba Joseph Kabila na jamhoriyar demokaradiyar Kwango ya amince da ziyarar António Guterres sakatare janar na MDD a daidai lokacin da Moussa Faki Mahamat shugaban kwamitin kungiyar tarayar Afirkan zai ziyarci kasar, inda za su tattauna kan yadda za a gudanar da zaben shugaban kasa gami da na 'yan Majalisu a kasar ta kwango.

Stephane Dujarric ya ce har yanzu ba a sanya ranar da za a gudanar da wannan tattaunawa ba, to amma idan aka yi la'akari da yanayin rikicin siyasar da kasar ke ciki, za a gudanar da tattaunawar ba da jimawa ba.

A ranar 22 ga watan Dicembar mai zuwa ne ake sa ran za a gudanar da zaben shugaban kasar ta Kwango kuma ya zuwa yanzu, shugaba Kabila bai bayyana aniyarsa na tsayawa takara ba.

Dage lokutan gudanar da zaben da shugaba kabila ya yi shi ne har so biyu ya janyo rikcin siyasa a kasar