Turai: Fiye Da Mutane 40 Suka Mutu Saboda Sanyi Mai Tsanani
https://parstoday.ir/ha/news/world-i28659-turai_fiye_da_mutane_40_suka_mutu_saboda_sanyi_mai_tsanani
Sanyi mai tsanani da saukar dusar kankara da ya mamaye kasashen turai ya ci rayukan mutane 41 mafi yawancinsu marasa gida
(last modified 2018-08-22T07:01:29+00:00 )
Feb 28, 2018 15:28 UTC
  • Turai: Fiye Da Mutane 40 Suka Mutu Saboda Sanyi Mai Tsanani

Sanyi mai tsanani da saukar dusar kankara da ya mamaye kasashen turai ya ci rayukan mutane 41 mafi yawancinsu marasa gida

Rahotannin da suke fitowa daga sassa daban-daban na nahiyar turai sun ambaci cewa adadin wadanda suka rasa rayukansu a kasashen Birtaniya da Hollanda sun kai 18, sai kuma wasu 6 a jamhuriyar Czech. A kasar Lithuania mutane biyar ne sanyin ya halaka sai kuma wasu mutane 4 a kasar Faransa. A kasar Slovakia mutum hudu sai Italia da Romania mutane bi-biyu.

Rufe hanyoyi da dusar kankara ta yi a cikin kasar Birtaniya ya yi sanadin hadarin mota da ya ci rayukan mutane.

An soka tashin jiragen sama da jiragen kasa da kuma rufe makarantu a cikin kasashen daban-daban na nahiyar ta turai.