Firaministan kasar Belgium ya ki amincewa da murabus din ministocinsa biyu
https://parstoday.ir/ha/news/world-i2872-firaministan_kasar_belgium_ya_ki_amincewa_da_murabus_din_ministocinsa_biyu
Ministocin cikin gida da na shara'ar kasar Belgium sun meka takarar murabus din su ga Firaminstan kasar sakamakon tagwayen hare-haren ta'addancin da aka kai ranar talatar da ta gabata.
(last modified 2018-08-22T06:58:01+00:00 )
Mar 24, 2016 10:50 UTC
  • Firaministan kasar Belgium ya ki amincewa da murabus din ministocinsa biyu

Ministocin cikin gida da na shara'ar kasar Belgium sun meka takarar murabus din su ga Firaminstan kasar sakamakon tagwayen hare-haren ta'addancin da aka kai ranar talatar da ta gabata.

Saidai Firaminstan kasar Charles Michel ya ki amincewa da murabus din na su, a cewar kamfanin dillancin labaran Reuteus sun yi ta kokarin jin martanin da ministan cikin gidan Jan Jambon da kuma Koen Geens ministan shara'ar kasar za su mayar amma lamarin ya cutura.

Yanzu haka dai magabatan kasar Belgium din na ci gaba da shan suka, tun bayan da Gwamnatin Turkiya ta sanar a jiya cewa shekarar da ta gabata ta kori Ibrahim Bakrawi daya daga cikin mutanan da suka kai harin birnin Brussels zuwa kasashen Turai tare da yiwa magabatan turan galgadin cewa mutum ne mai hadarin gaske.

A jiya Laraba ce Shugaban kasar Turkiya Rajab Tayyib Erdogan ya sanar da cewa magabatan kasar Belgium ba su dauki galgadin da ya yi musu da mahimancin ba ganin cewa Ibrahim Balkawi mutum ne mai tsaurin addini kuma mayaki ne da ya koyi dubarar yaki daga kasashen waje.

Tagwayen hare-haren da aka kai birnin Brusseles kwanaki biyu da suka gabata ya yi sanadiyar mutuwar mutane 34 yayin da sama da mutane 200 na daban suka jikkata.Kungiyar ISiS dai ta dauki alhakin kai harin.