Hadarin Jirgin Sama Ya Yi Ajalin Mutum 49 A Nepal
https://parstoday.ir/ha/news/world-i29021-hadarin_jirgin_sama_ya_yi_ajalin_mutum_49_a_nepal
Akalla mutane 49 ne aka tabbatar sun rasa rayukansu, in da 23 suka jikkata a hatsarin jirgin saman fasinjan a kusa da filin jirage na birnin Kathmandu da ke Nepal.
(last modified 2018-08-22T07:01:33+00:00 )
Mar 13, 2018 02:22 UTC
  • Hadarin Jirgin Sama Ya Yi Ajalin Mutum 49 A Nepal

Akalla mutane 49 ne aka tabbatar sun rasa rayukansu, in da 23 suka jikkata a hatsarin jirgin saman fasinjan a kusa da filin jirage na birnin Kathmandu da ke Nepal.

Hukumomin kasar sun bayyana hatsarin a matsayin mafi muni a kasar.

Hukumomi a Nepal sun ce, mutane 71 ne ke cikin jirgin saman na hadin gwiwar kamfanin Amurka da Bangladesh.

Kawo yanzu babu cikakken bayani game da musabbabin aukuwar hatsarin, amma wata sanarwa da hukumomi suka fitar ta ce, jirgin ya kubce wa matukinsa ne a yayin da yake dab da sauka.

Mai Magana da yawun kamfanin jirgin saman, Kamrul Islam, ya ce, 33 daga cikin fasinjojin ‘yan asalin kasar Nepal ne, yayin da 32 suka fito daga Bangladesh, sannan kuma akwai wani mutumin China guda da kuma dan asalin Maldives guda.

Hukumomin Nepal, sun sha alwashin gudanar da binciken gaggawa kan aukuwar hatsarin.