Kungiyar Kai Agaji Ta Bukaci Karin Ayyukan Jin Kai A Afrin
https://parstoday.ir/ha/news/world-i29228-kungiyar_kai_agaji_ta_bukaci_karin_ayyukan_jin_kai_a_afrin
Shugaban kungiyar bayar da agaji ta Red Cross ya bukaci kungiyoyin kai agaji da su kara kaimi na kai agaji ga al'ummar garin Afrin na kasar Siriya
(last modified 2018-08-22T07:01:35+00:00 )
Mar 19, 2018 15:31 UTC
  • Kungiyar Kai Agaji Ta Bukaci Karin Ayyukan Jin Kai A Afrin

Shugaban kungiyar bayar da agaji ta Red Cross ya bukaci kungiyoyin kai agaji da su kara kaimi na kai agaji ga al'ummar garin Afrin na kasar Siriya

Kamfanin dillancin labaran kasar Faransa ya nakalto Peter Maurer shugaban kwamitin kai agaji na Red Cross daga birnin ganeva na kasar Switzerland a wannan Litinin na cewa ci gaba da rikicin Afrin ya raba fararen hula da dama da mahalinsu, domin haka kungiyar Red Cross ta dauki nauyin ci gaba da kai agaji a yankin.

Yayin da ya koma kan yanayin da yankin ghouta ke ciki, mista Peter Maurer ya yabawa dakarun kasar Rasha kan rawan da suke takawa na kare fararen hula, sannan ya ce jami'an kungiyar kai agaji na Red Cross na kokari sosai wajen kwashe fararen hula da wadanda suka jikkata a yankin, sannan kuma ya bukaci sauren kungiyoyin kai agaji da su kara tura jami'ansu domin taimakawa fararen hula a yankin.

Daga ranar 20 ga watan Janairu da ya gabata lokacin da dakarun Turkiyya suka fara kaddamar da hari kan yankin na Afrin, dakarun kurdawa 1,500 ne aka kashe,  a yayin da Turkiyyar ta ce an kashe na ta dakaru 46 da raunana 225.