MDD:An Fitar Da Fararen Hula Dubu 45 Daga Yankin Ghouta
Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana cewa a cikin 'yan kwanakin nan, an fitar da fararen hula dubu 45 daya yankin Ghouta ta gabas a Siriya
Kamfanin dillancin labaran Reuteus ya habarta cewa Majalisar dinkin Duniya ta fitar da wani rahoto game da halin da yankin Ghouta ta gabas a Siriya ke ciki, inda ta ce a cikin kwanakin baya-bayan nan an fitar da fararen hula dubu 45 daga yankin.
A nasa bangare, Asusun dake kula da kananen yara na MDD Unicef a jiya talata ya sanar da cewa kashi 70% na mutanan da aka fitar daya yankin Ghouta Mata da kananen yara ne, kuma mafi yawa daga cikin yaran suna fama da rashin lafiyar gudawa da kuma matsalar limfashi.
A watan da ya gabata, kungiyoyin 'yan ta'adda da suka tare a yankin Ghouta dake gabashin Damuscus na Siriya suka yi ta harba makamai masu linzami kan fararen hula a Damuscus, lamarin da yayi sanadiyar mutuwa da kuma jikkata wani adadi mai yawa daga cikinsu, kuma hakan ya sanya gwamnatin ta Siriya daukan matakin kakkabe su daga yankin.