Trump Ya Yi Kalaman Tozarci Ga Saudiyya A Fakaice
Shugaban kasar Amurka Donald Trump ya yi kalaman tozarci ga Saudiyya a lokacin da yake ganawa da bakonsa saurayin yarima mai jiran gadon sarautar Saudiyya Muhammad Bin Salman a fadar white house.
A ganawar da ta gudana tsakanin shugaban Amurka Donald Trump da kuma yariman Saudiyya Muhammad Bin Salman a fadar white house, Trump ya bayyana Saudiyya matsayin babbar kwastoma ga Amurka, maimakon kiranta abokiyar kawancen Amurka.
Haka nan kuma Trump ya bayyana cewa a cikin 'yan lokutan nan sun karbi daruruwan biliyoyin dalolin Saudiyya na makaman da take saye daga Amurka, da kuma hannayen jarin da take ta sakawa a Amurka, wanda hakan a cewar Trump ya samar da ayyukan yi ga dubun dubatar Amurkawa.
Trump ya ce ko shakka babu Saudiyya kasa ce mai arziki da yawa, kuma yana fatan Saudiyya za ta bayar da wani bangaren arzikin nata ga Amurka, furucin da da dama daga cikin masana siyasar duniya suke kallonsa a matsayin tozarci ga kasar ta Saudiyya, babbar kasar da take kare manufofin siyasar Amurka da na kasashen yammacin turai baki daya a yankin gabas ta tsakiya.
Tun lokacin yakin neman zabe dai Trump ya kira kasar saudiyya a matsayin wata sanuwa mai madara da yawa da za a tatsa.