Kungiyar Ikhwanul Muslimin Ta Yi Kakkausar Suka Ga Kalaman Yariman Saudiyya
https://parstoday.ir/ha/news/world-i29730-kungiyar_ikhwanul_muslimin_ta_yi_kakkausar_suka_ga_kalaman_yariman_saudiyya
Kungiyar Ikhwanul Muslimin ta kasar Masar ta yi kakkausar suka ga kalaman yarima mai jiran gado na kasar Saudiyya kan kungiyar, inda ta bayyana kalaman nasa a matsayin tsagoron karya kana wani kokari na neman darewa karagar mulki ta hanyar neman goyon bayan Sahyoniyawa da Amurka.
(last modified 2018-08-22T07:01:40+00:00 )
Apr 08, 2018 06:18 UTC
  • Kungiyar Ikhwanul Muslimin Ta Yi Kakkausar Suka Ga Kalaman Yariman Saudiyya

Kungiyar Ikhwanul Muslimin ta kasar Masar ta yi kakkausar suka ga kalaman yarima mai jiran gado na kasar Saudiyya kan kungiyar, inda ta bayyana kalaman nasa a matsayin tsagoron karya kana wani kokari na neman darewa karagar mulki ta hanyar neman goyon bayan Sahyoniyawa da Amurka.

Kafar watsa labaran 'Al-Ahad' ta ba da rahoton cewa kungiyar Ikhwan din ta bayyana hakan ne a matsayin mayar da martani ga kalama Yarima Muhammad bn Salman din wanda ya bayyana kungiyar a matsayin kungiyar ta'addanci, inda ta ce karya ce tsagoronta yariman yake yi da nufin janyo hankulan sahyoniyawa da kuma Amurka don ya samu damar darewa karagar mulkin kasar Saudiyyan.

Har ila yau kungiyar ta Ikhwan, cikin wannan sanarwar da babban ofishin kungiyar ya fitar, ta ce ayyukan da shugabannin Saudiyya musamman Yarima Muhammad suke yi a halin yanzu, wani kauce wa hanya da kuma tunkuda mutane zuwa ga bata ne, bugu da kari kan hada musulmi fada, rufe ido kan masallacin Kudus da kokarin kulla alaka da haramtacciyar kasar Isra'ila.

Cikin 'yan kwanakin nan dai Yarima mai jiran gado na Saudiyyan yana ci gaba da shan suka sakamakon maganganun da yake yi na goyon bayan sahyoniyawa kan danyen aikin da suke yi a kan al'ummar Palastinu.