Faransa:Ci Gaba Da Adawa Na Sayarwa Saudiya Makamai
A yayin da yarima mai jiran gado na kasar Saudiya ke ziyara a kasar Faransa,an bukaci shugaban kasar Faransa da ya dakatar da sayarwa kasar ta saudiya makamai.
A yayin da Muhamad bn Salman yarima mai jiran gado na kasar Saudiya ke ziyara a kasar Faransa, masu rajin kare doka na jam'iyar Shugaba Macron sun bayyana cewa za su gudanar da bincike kan dokar sayarwa kawancen saudiya dae yaki a kasar Yemen da makamai.
Sebastian Nadu 'yan majalisar dokokin kasar Faransa kuma 'yar jam'iya mai milki tare da wasu 'yan majalisa 15, sun bukaci kafa kwamitin bincike kan yadda kasar ke sayarwa kasar Faransa makamai.
A cewar 'yan majalisar kasar ta Faransa, wannan kwamiti zai gudanar da bincike kan dokokin kasa da kasa na yadda kasar ke aikewa da makaman yaki da kuma taimakawa saudiya wajen ci gaba da kisan fararen hula a kasar Yemen.
Bisa wani bincike da cibiyar binciken You Gov ta gudanar, kashi 75% na al'ummar kasar Faransa na bukatar shugaba Macron ya dakatar da sayarwa Saudiya da hadaddiyar daular larabawa makamai.
Kasar Faransa dai na daga cikin manyan kasashen dake sayarwa kasar saudiya makamai.