Ma'aikatar Harkokin Wajen Rasha Ta Kirayi Jakadan Isra'ila A Moscow
https://parstoday.ir/ha/news/world-i29796-ma'aikatar_harkokin_wajen_rasha_ta_kirayi_jakadan_isra'ila_a_moscow
Ma'aikatar harkokin wajen kasar Rasha a yau ta kirayi jakadan Isra'ila a Moscow, domin neman karin bayani kan hare-haren da Isra'ila ta kaddamar a jiya a kan kasar Syria.
(last modified 2018-08-22T07:01:40+00:00 )
Apr 10, 2018 14:26 UTC
  • Ma'aikatar Harkokin Wajen Rasha Ta Kirayi Jakadan Isra'ila A Moscow

Ma'aikatar harkokin wajen kasar Rasha a yau ta kirayi jakadan Isra'ila a Moscow, domin neman karin bayani kan hare-haren da Isra'ila ta kaddamar a jiya a kan kasar Syria.

Kamfanin dillancin labaran sputink ya bayar da rahoton cewa, jakadan haramtacciyar kasar Isra'ila Gary Corn ya kai kansa a yau a babban ginin ma'aikatar harkokin wajen kasar Rasha a birnin Moscow, inda ya amsa tambayoyi daga mataimakin ministan harkokin wajen kasar kuma manzon musamman na shugaba Putin kan harkokin yankin gabas ta tsakiya Mikhail Bogdanov.

Babban jami'in na Rasha ya bukaci karin haske daga jakadan na Isra'ila dangane da harin da Isra'ila ta kai kan kasar Syria a jiya, da kuma kisan gillar da sojojin Isra'ila suka yi wa Palastinawa a Gaza a cikin wannan mako.

A jiya ne da jijjifin safiya Isra'ila ta kai kan filin jiragen sojin Syria a gundumar Homs, lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwar mutane tare da jikkatar wasu.