Babban Mataimakin Trump Kan Harkokin Tsaron Cikin Gida Ya Yi Murabus
https://parstoday.ir/ha/news/world-i29802-babban_mataimakin_trump_kan_harkokin_tsaron_cikin_gida_ya_yi_murabus
Majiyoyin fadar white house daga birnin Washington na Amurka sun ce, babban mataimakin shugaban kasar ta Amurka kan harkokin tsaron cikin gida Tom Bossert ya yi murabus daga kan mukaminsa.
(last modified 2018-08-22T07:01:41+00:00 )
Apr 10, 2018 14:28 UTC
  • Babban Mataimakin Trump Kan Harkokin Tsaron Cikin Gida Ya Yi Murabus

Majiyoyin fadar white house daga birnin Washington na Amurka sun ce, babban mataimakin shugaban kasar ta Amurka kan harkokin tsaron cikin gida Tom Bossert ya yi murabus daga kan mukaminsa.

Mai magana da yawun fadar White House Sara Sanders ce ta bayyana hakan a yau, inda ta ce tabbatar da cewa Tom Bossert ya sauka daga kan mukaminsa na babban mashawarcin Donald Trump kan harkokin tsaron cikin gida, amma ba ta yi wani karin bayani kan dalilin yin hakan ba.

A yau ne ake sa ran Tom Bossert zai kammala shiryawa wa Trump matakin da za su dauka kan zargin gwamnatin Syria da suke yi da yin amfani da makamai masu guba a kan yankin Douma da 'yan ta'adda suka mamaye.

Ko a jiya ma kakakin majalisar tsaron kasa a Amurka   Michael Anton ya mika takardar yin murabus daga aikinsa a karkashin gwamnatin Trump.

Daga lokacin da Trump ya karbi mulkin Amurka shekara guda da ta gabata ya zuwa yanzu, manyan jami'an gwamnatinsa da dama ne suka yi murabus daga aikinsu, tare da nuna rashin gamsuwa da salon shugabancinsa.