Alkawulan Gwamnatin Myanmar Ga Musulmi Yan Gudun Hijira Kasar A Bangladesh
Ministan walwala da jin dadin jama'a na kasar Myanmar ya ziyarci sansanonin yan gudun hijirar kasar da ke kan iyakar kasar da kasar Bangladesh, inda ya gana da wakilan yan gudun hijiran kimani 50 ya kuma shaida masu cewa batun kowarsu zuwa gida na daga cikin muhimman lamuran da gwamnatin kasarsa ta sa a gaba. Ya kuma kara da cewa gwamnatin kasar Myanmar tana duba batun basu takardun zama yan kasa.
Win Myat Aye ya yi wannan ganawar da wakilan yan gudun hijirar ne a lokacinda ya kai ziyarar aiki, a cikin yan kwanakin da suka gabata, a yankin kudu maso yammacin kasar ta Bangladesh, inda dubban daruruwan yan gudun hijirar kasarsa, suke samun mafaka.
Har'ila yau a ganawarsa da jami'an gwamnatin kasar Bangladesh Ministan walwala da jin dadin jama'a na kasar Myanmar ya shaida masu cewa, komarwa yan gudun hijira musulmi na kasarsa zuwa ginda yana daga cikin shirin gwamnatin kasar wanda kuma nan ba da dadewa ba zai tabbata.
Sai dai masana da dama suna ganin cewa, akwai abin dubawa cikin alkawarin da ministan ya yi, don wannan ba shi ne alkawali na farko wanda gwwamnatin kasar Myanmar take yiwa musulman Rokhinga na komawar gida ba.
A shekara ta 2017 da ta gabata, Priministan kasar Onga Son- Suchi, a wata ganawarta da ministan harkokin wajen kasar Bangladesh I.H. Mahmud Ali ta bayyana cewa gwamnatin na ta tana shirin maida yan gudun hijira musulmi yan kabilar Rokhinga zuwa gida nan ba da dadewa ba, amma yanzu kimanin watanni biyar Kenan, ba tare da an gani wani abu da ta yi na tabbatar da hakan ba.
Masana dai suna ganin cewa ziyarar da ministan walwala da jin dajin jama'a na kasar Myanmar ya kai kasar ta Bangladesh, ba ko me ba, in banda wani kokari ne na rage matsin lamban da kasashen yankin suke wa gwamnatin kasar, kan matsalar yan gudun hijira musulman Rokhinga, da kuma kokarin kaucewa zama saniyar ware a yankin.
Banda haka, wani abin mamaki dangane da matsayin gwamnatin kasar Myanmar kan komawar yan gudun hijirar Rokhinga zuwa gida, shi ne cewa, kafin ziyarar da ministan walwala da jin dadin jama'a na kasar ya kai kasar Bangladesh, gwamnatin kasar ta bada umurnin tsugunar da mabiyan addinin Buza yan kasar Bangladesh a yankunan da sojojinta suka kori musulman kasar a cikin kasar Myanmar.
Wannan ya nuna cewa, abinda gwamnatin take bayyana wa a fili, wata yaudara ce sannan makirci ne na ganin cewa musulman kasar yan kabilar Rokhinga basu sake komawa kasar ba.
Masana sun bayyana cewa gwamnatin kasar Myanmar ta fara aiwatar da wannan shirin ne tun shekara ta 2016 da ta gabata. Don haka batun maida musulman Rohinga zuwa gida wata yaudara ce ga kasashen duniya don ta kaucewa maida ita saniyar ware a duniya da kuma yankin.
Har'ila yau a wani bangaren kuma, shugaban hukumar kare hakkin yan gudun hijira ta kasa da kasa Mr Bill Freelick, ya bayyana cewa akwai bukatar gwamnatin Myanmar ta gudanar da wasu ayyuka masu muhimmanci a yankin Rokhin na kasar kafin a fara maganar komawar yan gudun hijirar gida, amma rahotonni da suke samu ya nuna cewa, har yanzun babu wani abu, wanda gwamnatin kasar ta gudanar a kasa wanda yake nuna cewa tana shirin maida yan gudun hijiran zuwa gida.
Shugaban hukumar yan gudun hijirar ya kara da cewa, dole ne kasashen duniya su tabbatar da cewa gwamnatin kasar Myanmar ta yi shirin komawar yan gudun hijiran Rokhinga kafin su amince da maidasu gida. Dole ne kasashen duniya su tabbatar da cewa gwamnatin kasar Myanmar zata bawa mutanen Rokhinta hakkokinsu na zama dan kasa, daga ciki har da kare lafiyansu, da kuma basu shaidar zama dan kasa da sauransu, kafin su koma gida.