An Fuskanci Koma Baya A Yaki Da Cutar Maleria
Apr 25, 2018 06:26 UTC
Yau 25 ga watan Afrilu, duniya ke bukin ranar yaki da cutar zazzabin cizon sauro ko Maleria.
Saidai bukin na bana ya zo a daidai lokacin da masana ke cewa an fuskanci koma baya a yaki da cutar, a 'yan shekaru uku da suka gabata.
Cutar da maleria dai ta fi kamari ne a kasashen nahiyar Afrika da kuma Asiya, kuma mafi yawa ta fi gallazawa yara da mata.
A taron da aka gudanar a birnin Landan a makon da ya gabata, kwararu sun bayyana dalilan habakar cutar da rashin ingancin magungunnan da ake warkar da ita da kuma yadda magungunan ke rage kayfiyarsu.