Ci Gaba Da Cin Zarafin 'Yan Jarida A Italiya
https://parstoday.ir/ha/news/world-i30316-ci_gaba_da_cin_zarafin_'yan_jarida_a_italiya
Rahoton da kungiyar 'yan jarida maras iyaka ta fitar na nuni da cewa Cin zarafin 'yan jarida ya karu a Italiya
(last modified 2018-08-22T07:01:45+00:00 )
Apr 26, 2018 14:35 UTC
  • Ci Gaba Da Cin Zarafin 'Yan Jarida A Italiya

Rahoton da kungiyar 'yan jarida maras iyaka ta fitar na nuni da cewa Cin zarafin 'yan jarida ya karu a Italiya

Kamfanin dillancin labaran Irna ta nakalto kungiyar 'yan jarida maras iyaka cikin wani rahoto da ta fitar a wannan alhamis na cewa kasar Italiya ta zamanto kasa ta 46 daga cikin cikin kasashen Duniya da suka amince da dokar 'yancin jaridu, da hakan ke nuna cewa ta dauki tazara mai yawa daga sauran kasashen Turai.

Rahoton ya ce cin zarafin da ake yiwa 'yan jarida ya karu a kasar Italiya  musaman ma a kudancin kasar.

Kungiyar 'yan jarida maras iyaka ta ce 'yan jaridun kasar Italiya na fuskantar matsin lamba daga kungiyoyin 'yan mafiya na kasar, duk da cewa ba a cika kai muku hari kai tsaye ba, amma ana shiga cikin gidajensu, sannan awan gaba da wasu mahiman bayanai da suke da shi tare kuma da kwace musu na'ura mai kwakwaluwa da suka amfani da su.