Iran Ta Mayar Da Martani Ga Barazanar Jami'an H.K. Isra'ila
https://parstoday.ir/ha/news/world-i30340-iran_ta_mayar_da_martani_ga_barazanar_jami'an_h.k._isra'ila
Jakadan Iran na dindindin a Majalisar Dinkin Duniya, Gholamali Khoshroo, ya bayyana cewar haramtacciyar kasar Isra'ila ta tabbatar da yanayinta na wuce gona da zalunci kana kuma ita ce ummul aba'isin din dukkanin rikice-rikicen da ke faruwa a yankin Gabas ta tsakiya.
(last modified 2018-08-22T11:31:45+00:00 )
Apr 27, 2018 16:06 UTC
  • Iran Ta Mayar Da Martani Ga Barazanar Jami'an H.K. Isra'ila

Jakadan Iran na dindindin a Majalisar Dinkin Duniya, Gholamali Khoshroo, ya bayyana cewar haramtacciyar kasar Isra'ila ta tabbatar da yanayinta na wuce gona da zalunci kana kuma ita ce ummul aba'isin din dukkanin rikice-rikicen da ke faruwa a yankin Gabas ta tsakiya.

Jakadan Iran din a MDD ya bayyana hakan ne cikin wata sanarwa da ya aike wa Kwamitin Tsaron MDD dangane da irin barazanar da jami'an HKI suke ci gaba da yi na kai hare-hare kan wasu kasashen Gabas ta tsakiya ciki kuwa har da Iran da Siriya inda ya ce wadannan maganganu suna nuni ne da irin dabi'ar wuce gona da iri, mamaya da zaluncin haramtacciyar kasar Isra'ilan.

Har ila yau jakadan na Iran yayi kakkausar suka ga Amurka da sauran membobin Kwamitin Tsaron wadanda suke ci gaba da daure wa "Isra'ilan" baya wajen aikata danyen aikin da take ci gaba da yi kan kasashen yankin Gabas  ta tsakiyan wanda hakan ke ci gaba da sanya tsaron yankin cikin hatsari.

Sanarwar dai ta biyo bayan wasu barazanar kai hare-hare kan wasu kasashe ne, ciki kuwa har da Iran da Siriya, da jami'an 'Isra'ilan' suke ci gaba da yi wanda Kwamitin Tsaron yayi guma da bakinsa kansu.

A jiya ne dai ministan 'tsaron' Isra'ila  Avigdor Liberman a wata hira da yayi da kafar watsa labaran Elaph na kasar Saudiyya yayi barazanar kai wa kasar Iran da kuma cewa ba za su taba bari Iran ta samin gindin zama a Siriya ba, lamarin da jami'an Iran da dama suka ja kunnensu kan hakan.