Kungiyar EU Ta Goyi Bayan Tattauwar Shugabannin Korea Biyu
https://parstoday.ir/ha/news/world-i30348-kungiyar_eu_ta_goyi_bayan_tattauwar_shugabannin_korea_biyu
Babbar jami'ar harkokin wajen kungiyar tarayyar turai ta bayyana goyon bayan kungiyar EU ga tattaunawar da shugabannin kasashe korea ta arewa da korea ta kudu suka yi a jiya juma'a.
(last modified 2018-08-22T07:01:45+00:00 )
Apr 28, 2018 01:53 UTC
  • Kungiyar EU Ta Goyi Bayan Tattauwar Shugabannin Korea  Biyu

Babbar jami'ar harkokin wajen kungiyar tarayyar turai ta bayyana goyon bayan kungiyar EU ga tattaunawar da shugabannin kasashe korea ta arewa da korea ta kudu suka yi a jiya juma'a.

Kamfanin dillancin labaran Irna ya nakalto Babbar jami'ar harkokin wajen kungiyar tarayyar turai Federica Mogherini na cewa tattaunawar da shugabannin kasashen Korea ta kudu da korea ta arewa suka yi shi ke nuna cewa duk da irin matsalolin dake tsakanin kasashen biyu, to amma akwai yiyuwar sulhu a tsakanin su.

Jami'ar ta kara da cewa tattaunawa ita ce hanya mafi kyau na samar da hanyar  sulhu da kuma warware matsala , wannan kuma shi ne amfanin yankin da duniya gaba daya.

Har ila yau uwar gida Federica Mogherini ta ce kungiyar EU a shirye take ta karbi duk wata bukata na shugabanin kasashen biyu, da makance matsalar makaman kare dangi a yankin.

Da sanyin safiyar jiya juma’a ce aka gudanar da ganawar tarihi kusa da iyakokin kasashen biyu, shugabannin Korea ta Arewa da Korea ta Kudu sun gudanar da liyafar cin abincin rana a tare.

Wannan dai shi ne karo na uku a cikin shekaru 65 da shugabannin kasashen biyu da ba sa ga maciji  ke ganawa da juna da nufin warware tsohuwar kiyayyar da ke tsakaninsu, wadda ta samo asali daga bambancin ra’ayi na siyasa.