An Kashe Dan Jaridar BBC A Afganistan
A marecen yau wasu 'yan bindiga sun bindigar dan jaridar BBC a jahar Houst dake kasar Afganistan.
Kamfanin dillancin labaran kasar Iran daga Birnin Kabul ya habarta cewa a marecen wannan litinin wasu 'yan bindiga sun bindiga Ahmad Shah dan jaridar BBC bangaren Fashtu a jahar Houst dake gabashin kasar.
Wannan dai shine dan jarida na goma da aka kashe yau a birnin Kabul da jahar Houst a kasar ta Afganistan,
A wasu tagwayen hare- haren Bam da aka kai safiya yau a birnin Kabul ya yi sanadiyar mutuwar mutane 40 cikin kuwa har 'yan jaridu da masu daukan Hoto guda tara daga cikin 'yan jaridun da suka hallaka har da Shah Marai dan jarida mai daukar hoto na kafar yada labaran Faransa AFP.
har ila yau rahoton ya ce daga cikin mutunan da suka rasa rayukansu akwai kananen yara 11 yayin da wasu takwas na daban suka samu mumunan rauni.
Tuni dai kungiyar ta'addancin nan ta Da'esh ta dauki alhakin kai harin.