Putin Da Macron Sun Tabbatar Da Kiyaye Yarjejjeniyar Nukiliyar Iran
Shugabanin kasashen Rasha da Faransa sun tattauna ta hanyar talho kan mahimancin kiyaye yarjejjeniyar nukiliyar Iran.
Cikin wata sanarwa da fadar shugaban kasar Rasha ta fitar ta ce a wannan Litinin Shugaba Viladimin Putin da takwaransa na Faransa Emanuel Macron sun tattauna ta hanyar talho kan yarjejjeniyar nukiliyar zaman lafiya da kasar Iran ta cimma tare da manyan kasashe biyar da kasar Jamus.
A yayin tattaunawar, shugaban kasar Faransa ya bayyanawa shugaba Putin sakamakon ziyarar baya-bayan da ya kai kasar Amurka musaman ma kan tattaunawar da suka yi da shugaba Trump kan yunkurin ficewar da kasar Amurka take yi daga yarjejjeniyar nukiliyar zaman lafiya na kasar Iran.
Kafin hakan dai, Shugabar gwamnatin Jamus Angela Markel da shugaban kasar Faransa Emanuel Macron da Piraministan kasar Birtaniya Theresa May sun bayyana cewa a shirye suke su sake tattaunawa kan yarjejjeniyar nukiliyar da suka cimma da kasar Iran.
Sa'o'i kafin fitar da wannan sanarwa na wadannan shugabani, Shugaban kasar Iran Dakta Hasan Rauhani ya tabbatar da cewa babu batun sake tattaunawa kan yarjejjeniyar nukiliyar zaman lafiya da kasar ta cimma da manyan kasashen Duniya 5 gami da kasar Jamus.
Yanzu dai Shugaban na Amurka na wa'adi zuwa 12 ga watan Mayu mai kamawa wajen bayyana ra'ayinsa na ficewa ko kasancewa tare da wannan yarjejjeniya.