Hatsarin Jirgin Sama Ya Yi Ajalin Mutum 100 A Cuba
Rahotanni daga Cuba na cewa, mutane a kalla 100 ne suka gamu da ajalinsu bayan da wani jirgin sama kirar Boeing 737 ya rikito kusa da filin jirgin sama na Jose Marti International da ke Havana, babban birnin kasar.
Bayanai daga kasar sun ce akwai mutum uku da suka tsira daga hadarin jirnin na jiya Juma'a, saidai suna cikin mawuyacin hali.
Jirgin dai na kamfanin ''Cubana de Aviacion'' mai dauke da fasinjiji 104, da mambobinsa 6 ya fado ne jin kadan bayan tashinsa a wani wuri da ba mazauna jim kadan bayan tashinsa daga filin jirnin na Havana zuwa Holguin.
Shugaban kasar Miguel Diaz-Canel, wanda ya isa wajen da jirgin ya yi hadari, ya ce lamarin bashi da dadin ji, an samu hasara rayuka masu yawa.
Tuni dai hukumomin kasar suka ayyana zaman makoki na kwanaki biyu daga yau Asabar.