Yawan Mutanen Da Suka Rasa Rayukansu A Gwatamala Ya Kai 69
Yawan mutanen da suka rasa rayukansu a aman wuta na tsaunukan Fuego a kasar Gwatemala ya kai 69 bayan da wata girgizan kasa mai karfin ma'aunin Rechter 5.2 ya aukawa yankin kudu maso yammacin kasar a jiya litinin.
Tashar talabijin ta RT ta kasar Rasha ta nakalto hukuma mai kula da girgizan kasa ta duniya wato Geological Survey a kasar Amurka tana tabbatar da labarin ta kuma kara da cewa girgizan kasar ta auku ne kilomita 105 daya lardin Champerico mai makubtaka da tsunukan na Fuego.
Labarin ya kara da cewa har yanzun ba'a tantance irin yawan asarorin da girgizan kasar ta jawo ba, amma dai an yi ta jin karar facewar abubuwan a duk tsawon ranar jiya litinin.
A wani bangare kuma shugaban kasar ta Gwatemala Jimmy Morales ya shelanta doka da baci a yankin, ya kuma bayyana cewa ma'aikatan agaji 1,200 ne suka fara aikin ceto a yankin. Sannan ya bukaci mutanen yankin su dai na sauraron jita-jita dangane da lamarin aman wutan.