Taron G7 Ya Kara Hadin Kai Tsakanin Kasashen Kasashen Turai.
Ministan tattalin arziki na kasar Jamus Peter Altmaier ya bayyana cewa taron G7 a kasar Canada ya kara hada kan kasashen turai don fuskantar mummunar siyasar shugaban kasar Amurka Donal Trump
Kamfanin dillancin labaran reuters ya nakalto Peter Altmaier yana fadar haka a jiya Litinin, a taron ministocin makamashi na kasashen tarayyar Turai, ya kuma kara da cewa taron manya manyan kasashen duniya masu arzikin masana'antu a duniya wanda ake kira G7 ya kara kusantar da kasashen turai a tsakaninsu.
Shugaban kasarb Amurla Donal Trump wanda ya bar taron na G7 kafin lokacin kammala shi ya ki sanya hannu a kan takardan bayan taro na taron don wasu abubuwan da aka shigo da su cikinsa wanda bai amince ba.
An gudanar da taron G7, wanda ya tattara manya kanyan kasashen duniya 7 masu karfin masana'antu, wadanda kuma suka hada da Amurka, Jamus, Britania, Faransa, Italiya da Japan a birnin Quebec na kasar Canada.
Kasashen na turai sun yi alkawarin maida marati ga matakan da shugaban kasar Amurka ya dauka na kara haraji kan bakin karfe da karfen alminuim wadanda ake shigo da su Amurka daga kasashen na turai, inda hakan ya sabawa yerjejeniyar budaddiyar kasuwan duniya da suka amince da iya.