Musulmai Na Bikin Karamar Sallah
(last modified Fri, 15 Jun 2018 03:29:47 GMT )
Jun 15, 2018 03:29 UTC
  • Musulmai Na Bikin Karamar Sallah

Al'ummar Musulmi a galibin kasashen duniya na bikin Eid al-Fitr ko kuma karamar Sallah bayan kamalla azumin watan Ramadana.

Eid al-Fitr na daga cikin bukukuwan ibada mafi girma a tsakanin al'ummar Musulmi.

Ana dai bukukuwan ne bayan hango jinjirin watan Sawwal wanda ya kawo karshen watan azumin Ramanada, wato daya daga cikin shika-shikan musuluncin nan guda biyar.

A nan Jamhuriya musulinci ta Iran ma a yau ne ake gudanar da Sallar ta Eid al-Fitr, kamar yadda take gudana a kasashen Saudiyya, Najeriya, da dai sauren kasashen Musulmi.

Tun a jiya ne dai wasu kasashen da suka hada da Nijar, suka yi tasu sallar bayan hangen jinjirin watan na Shawwal.

A lokaci irin wannan dai Musulmi kan tafi Sallar Idi, bayan nan ne kuma suke ci gaba da taya juna murna ta hanyar ziyarce-ziyarce da kuma wasu nau'o’in nishadi.