Shugaban Babban Bankin Kasar Argentina Ya Yi Murabus Daga Kan Mukaminsa
Bayan bullar matsalar ci gaba da faduwar darajar kudin Argentina, shugaban babban bankin kasar ya dauki matakin yin murabus daga kan mukaminsa.
Duk da matakan da aka dauka na ganin an shawo kan matsalar ci gaba da faduwar darajar kudin Argentina musamman yarjejeniyar da gwamnatin kasar ta cimma da asusun bada lamuni na duniya amma matsalar faduwar darajar kudin tana ci gaba da gudana, hakan ya sanya shugaban babban bankin kasar ta Argentina Federico Sturzenegger ya yi murabus daga kan mukaminsa.
A wani bayani da gwamnatin Argentina ta fitar yana nuni da cewa: Kimar kudin kasar peso yana ci gaba da faduwa a gaban dalar Amurka, inda a cikin kwana guda kacal an samu faduwar kimar da kashi shida cikin dari.
Bayan murabus din Federico Sturzenegger wanda masani ne a harkar tattalin arziki, Luis Caputo ministan kudin kasar ta Argentine ne ya karbi ragamar shugabancin babban bankin kasar.