Zaman Kwamitin Tsaron MDD Kan Rikicin Yemen
https://parstoday.ir/ha/news/world-i31856-zaman_kwamitin_tsaron_mdd_kan_rikicin_yemen
Kwamitin tsaron majalisar dinkin duniya ya jaddada wajabcin warware matsalar rikicin Yemen ta hanyar tattaunawar siyasa.
(last modified 2018-08-22T07:02:00+00:00 )
Jun 19, 2018 14:53 UTC
  • Zaman Kwamitin Tsaron MDD Kan Rikicin Yemen

Kwamitin tsaron majalisar dinkin duniya ya jaddada wajabcin warware matsalar rikicin Yemen ta hanyar tattaunawar siyasa.

Mataimakin jakadan Rasha a majalisar dinkin duniya da ke jagorantar shugabancin kwamitin, ya bayyana cewa wajibi a tabbatar da cewa tashar ruwa ta Hudaida ba ta fita daga aiki ba, domin kuwa ita kadai ce hanyar isa da agaji ga al'ummar yemen.

Martin Griffiths manzon musamman na majalisa dinin duniya kan rikicin Yeman, ya gabatar wa kungiyar Ansarullah shawara ne kan ta janye daga gabar ruwan Hudaida, amma kungiyar taki amincewa da hakan, saboda rashin tabbaci dangane da makomar wannan gabar ruwa, domin kuwa kungiyar ta bayyana cewa tana yaki ne da sojojin Amurka da na faransa da Birtaniya da suke yi wa Saudiyya yaki a Hudaida.

Kungiyar ta ce za ta sanar da shawar da ta yanke bayan tatatunawa da wasu bangarori kan batun, amma ba za su bari Saudiyya da Amurka su mamaye wannan gabar ruwa ba.