Turai Za Su Tattauna Da Amurka Domin Kawo Karshen Yakin Kasuwanci
Babbar Jami'a mai kula da harkokin kasuwancin na Tarayyar turai Cecilia Malmstrom ta fada a yau alhamis cewa; Tarayyar Za ta bude tattaunawa da Amurka domin warware jayayyar da suke yi akan karin kudin fito akan hajar kasuwanci
Babbar jami'ar ta Tarayyar Turai din ta ci gaba da cewa; An yanke wannan shawarar ta tattauanwa ce bayan da Amurkan ta kara kudin ifto akan karafa da alminium da take saya daga tarayyar turai.
Cecilia Malmström ta ci gaba da cewa; Wajibi ne ga kungiyar kasuwancin ta duniya da ta gudanar da bincike akan batun kasuwanci na kasar Sin da yadda hajojin da kasar take kerawa suka fado.
A cikin watan Maris ne shugaban kasar Amurka ya kara kaso 25% na kudin fito akan karafa da kuma kaso 10% akan sarfen Uranium. Sai dai shugaban na Amurka ya yi alkawalin dage wa wasu kasashen turai din kudaden fiton na dan wani lokaci