Sarauniyar Ingila Ta Amince Da Ficewar Britania Daga Tarayyar Turai
Kakakin majalisar dokokin kasar Britania ya bada sanarwan cewa ficewar kasar daga tarayyar Turai ta zama doka bayan da sarauniyar kasar ta amine da batun kamar yadda mutanen kasar suke bukata.
John Bercow ya fadawa yan majalisar dokokin kasar a yau talata kan cewa sarauniya Elizabeth11 ta amince da ficewar kasar daga tarayyar Turai, don haka a halin yanzu batun ficewar Britani daga tarayyar Turau ta zama doka.
Kafin haka dai Firaiministan kasar Theresa May ta fuskanci matsaloli da dama a majalisun dokokin kasar kafin batun ya wuce. Ta kuma bayyana cewa samun amincewar Sarauniyar zai kara sawwaka sauran ayyukan ficewa daga kungiyar.
May ta bayyana cewa wannan wani babban abu ne a tarihin kasar Britani, kuma abubuwan da suka rage na kammala ficewar kasar daga tarayyar ta Turai masu sauki ne.
Har'ila yau amincewar sarauniyar ya kawo karshen dokar da ta amincewar kasar shiga tarayyar ta Turai a shekara 1972. A ranar 23 ga watan Yuni shekara ta 2016 ne aka gudanar da zaben raba gardama a kasar ta Britani inda sakamansa ya nuna cewa mutanen kasar sun zabi ficewa daga tarayyar ta Turai da karamin rinjaye na kashi 51.9%.