MDD Ta Gano Gidajen Kaso Na Sirri A Yemen
https://parstoday.ir/ha/news/world-i32188-mdd_ta_gano_gidajen_kaso_na_sirri_a_yemen
MDD Ta Tabbatar da cewa hadaddiyar daular larabawa nada wani gidan Kaso na sirri a kasar Yemen inda take azabtar tare da cin zarafin Mata a cikinsa.
(last modified 2018-08-22T07:02:03+00:00 )
Jul 04, 2018 07:24 UTC
  • MDD Ta Gano Gidajen Kaso Na Sirri  A Yemen

MDD Ta Tabbatar da cewa hadaddiyar daular larabawa nada wani gidan Kaso na sirri a kasar Yemen inda take azabtar tare da cin zarafin Mata a cikinsa.

Kafar watsa labaran Al-ahad ta nakalto Elizabeth Trossel kakakin babban kwamishinan hukumar kare hakin bil-adama ta MDD na cewa akwai shedu a hanunmu dake nuni da cewa dakarun tsaron hadaddiyar daular larabawa na azabtar da 'yan kaso a kasar yemen sannan kuma suna yiwa mata fyade a cikinsa.

Trossel ta tabbatar da cewa shidai wannan gidan kaso na sirri ne da hadaddiyar daular larabawa ne kula da shi, 

Elizabeth Trossel ta ce duk da cewa mun tattauna da magabatan Hadaddiyar daular larabawa a kan su bamu damar ziyartar wannan gidan kaso, amma har yanzu sun ki su bayar da izinin hakan.

A baya-bayan nan dai an watsa rahoton cewa akwai gidajen Kaso 18 a kudancin kasar Yemen da gwamnatin hadaddiyar daular larabawa ke kula da su, kuma taki bayar da izini ga ko wata hukuma ta kasa da kasa kai ziyara a cikinsu.