Kasar Amurka Ta Kakaba Takunkumi Kan Wasu Jami'an Gwamnatin Kasar Nicaragua
https://parstoday.ir/ha/news/world-i32209-kasar_amurka_ta_kakaba_takunkumi_kan_wasu_jami'an_gwamnatin_kasar_nicaragua
Ma'aikatar Baitun Malin Kasar Amurka ta kakaba takunkumi kan wasu jami'an kasar Nicaragua kan zargin take hakkin bil-Adama a kasarsu.
(last modified 2018-08-22T07:02:04+00:00 )
Jul 06, 2018 02:08 UTC
  • Kasar Amurka Ta Kakaba Takunkumi Kan Wasu Jami'an Gwamnatin Kasar Nicaragua

Ma'aikatar Baitun Malin Kasar Amurka ta kakaba takunkumi kan wasu jami'an kasar Nicaragua kan zargin take hakkin bil-Adama a kasarsu.

A wata sanarwa da ma'aikatar Baitul Malin Kasar Amurka ta fitar ta bayyana cewa: Takunkumin da ta kakaba kan jami'an gwamnatin kasar Nicaragua ya hada da Francisco Javier Diaz Madriz daya daga cikin manyan jami'an rundunar 'yan sandan Nicaragua da Fidel Antonio Morino babban jami'i a ma'aikatar Magajin garin birnin Managua fadar mulkin kasar gami da Jose Francisco Lopez shugaban wani kamfanin man fetur na kasar ta Nicaragua.

Kasar Amurka dai ta dauki wannan mataki ne na kakaba takunkumi kan jami'an na Nicaragua kan zargin cewa suna da hannu a take hakkin bil-Adama a kasarsu musamman murkushe 'yan adawa.

Tun a tsakiyar watan Aprilun wannan shekara ce 'yan adawa a Nicaragua suka yunkuro ta hanyar gudanar da zanga-zanga babu kakkautawa da nufin ganin bayan gwamnatin Daniel Ortega, inda dauki ba dadi tsakanin 'yan adwar da jami'an tsaron kasar ya lashe rayukan mutane fiye da 180.