Paparoma Ya Bukaci Duniya Ta Taimakawa 'Yan Gudun Hijira
https://parstoday.ir/ha/news/world-i32220-paparoma_ya_bukaci_duniya_ta_taimakawa_'yan_gudun_hijira
Paparoma Francis Shugaban darikar Catolica ya bukaci kungiyoyin kasa da kasa da su ceci rayukan bakin haure a gabar tekun ruwan kasashen Turai.
(last modified 2018-08-22T07:02:04+00:00 )
Jul 07, 2018 01:49 UTC
  • Paparoma Ya Bukaci Duniya Ta Taimakawa 'Yan Gudun Hijira

Paparoma Francis Shugaban darikar Catolica ya bukaci kungiyoyin kasa da kasa da su ceci rayukan bakin haure a gabar tekun ruwan kasashen Turai.

A jiya juma'a, ofishin Paparoma Francis na cocin Catholica ya bayyana damuwa a kan yadda ake ci gaba da rikici a sassa daban daban na Duniya, sannan ya ce wajibi ne a taimakawa 'yan gudun hijra da suka baro kasashensu suka kuma bukaci taimako a gare mu.

Cikin jawabinsa Paparoma ya ce matakin da gwamnatin Italiya ta dauka na hana jiragen ruwan kungiyoyin dake aikin alheri masu dauke da bakin haure ya janyo wa kasar takun saka tsakaninta da makwabtanta cikinsu har da Faransa.

A bangare guda, Paparoma ya bukaci 'yan gudun hijrar da su mutunta al'adu da dokokin kasashen da suka karbe su.

Kafin hakan dai, Ministan cikin gidan kasar Italiya kuma mataimakin Piraministan kasar ya sha nanata cewa ba za su sake bayar da dama ga jiragen ruwan bakin haure shiga tashar jiragen ruwa na kasar ba, daga lokaci da gwamnati ta dauki wannan mataki, duk wani jirgin ruwa dake dauke da 'yan gudun hijra ko na wata kungiya ce, ba za a amince da shi ba, saidai ya fice wata kasar ta daban.