Kofin Duniya:Uruguay Da Brazil Sun Kasa A Gaban Wakilan Turai
https://parstoday.ir/ha/news/world-i32221-kofin_duniya_uruguay_da_brazil_sun_kasa_a_gaban_wakilan_turai
A Ci gaba da gasar cin kofin kwallon kafa na Duniya Rasha 2018, tawagogin kwallon kafa na Uruguay da Barazil sun sha kashi a hanun takwarorinsu na Faransa da Belgium
(last modified 2018-08-22T07:02:04+00:00 )
Jul 07, 2018 01:51 UTC
  • Kofin Duniya:Uruguay Da Brazil Sun Kasa A Gaban Wakilan Turai

A Ci gaba da gasar cin kofin kwallon kafa na Duniya Rasha 2018, tawagogin kwallon kafa na Uruguay da Barazil sun sha kashi a hanun takwarorinsu na Faransa da Belgium

A marecen jiya juma'a ne aka buga kwallon kafa tsakanin tawagar kwallon kafa na Faransa da Uruguay da faransa, inda kasar Faransa ta doke Uruguay din da ci 2-0, ita ma kasar Belgium ta doke kasar Brazil da ci 2-1, da hakan ya basu damar tsallake zuwa zagayen dab da na karshe a gasar cin kofin duniya.

Karo na farko kenan da Faransa ta samu nasara wajen kai wa matakin kusa da na karshe a gasar ta cin kofin duniya tun bayan shekarar 2006.

Yanzu Belgium za ta hadu ne da makwabciyarta Faransa a zagayen dab da karshe a ranar Talata 10 ga watan Yuli.

Karon farko ke nan a tarihi da kasashen Turai guda hudu za su buga wasan dab da na karshe.

Wasa tsakanin Sweden da Ingila da kuma wasa tsakanin Rasha da Croatia da za su buga a marecen yau Asabar, dukkaninsu daga Turai za su iya tsallakewa zuwa zagayen dab da karshe.