Sakataren Harkokin Wajen Kasar Birtaniya Ya Yi Murabus Daga Kan Mukaminsa
https://parstoday.ir/ha/news/world-i32259-sakataren_harkokin_wajen_kasar_birtaniya_ya_yi_murabus_daga_kan_mukaminsa
Ofishin fira ministar kasar Birtaniya ya sanar da cewa: Sakataren harkokin wajen kasar Boris Johnson ya yi murabus daga kan mukaminsa.
(last modified 2018-08-22T07:02:05+00:00 )
Jul 09, 2018 13:49 UTC
  • Sakataren Harkokin Wajen Kasar Birtaniya Ya Yi Murabus Daga Kan Mukaminsa

Ofishin fira ministar kasar Birtaniya ya sanar da cewa: Sakataren harkokin wajen kasar Boris Johnson ya yi murabus daga kan mukaminsa.

A sanarwar da ofishin fira ministan kasar Birtaniya ya fitar ya fayyace cewa: Sakataren harkokin wajen kasar Boris Johnson ya yi murabus daga kan mukaminsa a yammacin yau Litinin, kuma fira ministar kasar Theresea May ta amince da murabus din nasa tare da jinjina masa kan irin gudumawar da ya gabatar a gwamnatinta.

Murabus din Boris Johnson ya zo ne bayan sa'o'i kadan da David David ya ajiye mukaminsa na minista mai kula da harkokin yarjejeniyar ficewar kasar Birtaniya daga cikin kungiyar tarayyar Turai, kuma dukkanin ministocin biyu sun yi murabus ne daga kan mukamansu sakamakon rashin amincewarsu da tsare-tsaren da fira ministar kasar Theresa May take son gudanarwa a alakar kasarta da kungiyar tarayyar Turai bayan kammala ficewar kasarta daga kungiyar a hukumance lamarin da ministocin biyu suke ganin shirin nata ya yi hannun riga da manufar al'ummar Birtaniya ta ficewa daga cikin kungiyar ta tarayyar Turai.

Ofishin fira ministar ta Birtaniya ta bayyana cewa: A nan gaba kadan za a sanar da mutumin da zai maye gurbin Boris Johnson a matsayin sabon sakataren harkokin wajen kasar.