Jeremy Hunt Ya Zama Sakataren harkokin Wajen Kasar Britania.
Ofishin Priministan kasar Pritania ya bada sanarwan nada Jeremy Hunt a matsayin sabon sakataren harkokin wajen kasar bayan murabus din da Boris Johnson yayi a jiya litinin.
Kamfanin dillancin labaran IRNA na kasar Iran ya kara da cewa ofishin Priministan har'ila yau ya bada sanarwan cewa kafin wannan sabon matsayin da aka bashi, Jeremy Hunt shi ne sakataren kiwon lafiya. Banda haka Priministan ta nada Matt Hancock a matsayin sabon sakataren kiwon lafiya.
Kafin murabus din da Boris Johnson ya yi a jiya Litinin dai sakataren shirin ficewar Britania daga tarayyar Turai David Davis ya ajiye mukaminsa. Wadannan sakatarorin dai sun ajiye mukamansu ne don nuna rsashin amincewarsu da tsarin Priminista Theresa May na wanzar da wani bangaren da dangantakar Britania da tarayyar Turai bayan ficewar kasar daga tarayyar ta Turai.