Tsangwamar Larabawa Na Dada Karuwa A Amurka
Wata cibiyar Labarawa da ke birnin Washington ta yi ikirarin cewa akwai karuwar cin zarafin Larabawa a Amurka.
Rahoto na cibiyar Larabawa Amurkawa da ke Washington ya ce yawan cin zarafin Larabawa da aka yi tsakanin 2015 da 2016 ya ribanya adadin da hukumar bincike ta FBI ta bayyana.
Cibiyar ta ce hakan na nuni da irin raunin da ke tattare da kididdigar hukumar ta FBI, a daidai lokacin da ake samun karuwar laifukan nuna tsana a kasar.
Rahoton na cibiyar ya kawo misali, da kashe wasu matasa Larabawa 3 da aka yi daura da Jami'ar North Carolina a 2015.
Bayan nazarin bayanai daga hukumomin tsaron jahohi, cibiyar ta yi kiyasin cewa an fuskanci take-taken tsanar Larabawa a Amurka har sau 79 a shekarar 2015, a maimakon guda 40 da hukumar FBI ta bayyana; da kuma sau 88 a 2016 a maimakon 58 da aka bayyana a rahoton na FBI.