Za'a Fuskanci Khusufin Wata Mafi Tsawo A Yau Juma'a
https://parstoday.ir/ha/news/world-i32498-za'a_fuskanci_khusufin_wata_mafi_tsawo_a_yau_juma'a
A wani lokcai yau Juma'a ne za'a fuskanci khusufin rana mafi tsawo.
(last modified 2019-03-07T02:07:59+00:00 )
Jul 27, 2018 01:00 UTC
  • Za'a Fuskanci Khusufin Wata Mafi Tsawo A Yau Juma'a

A wani lokcai yau Juma'a ne za'a fuskanci khusufin rana mafi tsawo.

Saidai ba a ko ina ne a duniya za'a fuskanci khusufin ba, ko zazzabin watan ba, wanda wasu suke cewa ''rana ya kama wata''.

Za'a ga khusufin ne a gabadayan shi a gabashi da tsakiya da kudancin Afrika, da gabas ta tsakiya na kasar Indiya da kuma Asiya ta tsakiya, da kuma Antactica.

Yankunan kudancin Amurka, da Turai da Afrika ta yamma zasu ga karshen khusufin ne, a yayin da bangaren China da galibin Rasha zasu ga farkon khusufin ne kawai, a yayin da ba za'a ganshi ba a Arewacin Amurka da tsakiyarta ba.

Masana sararin samaniya dai na danganta khusufi da lokacin da rana da duniya da kuma wata suka jeru a sahu guda,  a yayin da duniya kan yi wa wata inuwa, wanda ke hana hasken rana fadawa kan wata na dan wani lokaci.

Amma hakan kuma yana da tasa fahintar a wasu addinai da al'adu, a yayin da wasu kuma ke kallonsa a matsayin bala'i.