Yan Adawar Kasar Nicaragua Kimanin 600 Ne Suka Bace Babu Labarinsu
Cibiyar kare hakkin bil-Adama ta kasar Nicaragua ta ce daruruwan 'yan adawar kasar sun bace babu labarinsu tun bayan da jami'an tsaro suka yi awungaba da su a yankin kudancin birnin Managua fadar mulkin kasar.
Cibiyar kare hakkin bil-Adama ta Nicaraguan Human Rights Center a jiya Alhamis ta fitar da sanarwar cewa: 'Yan adawar Nicaragua kimanin 600 ne suka bace babu labarinsu bayan da jami'an tsaron kasar suka yi awungaba da su a lokacin da suka fito zanga-zangar nuna kiyayya ga gwamnatin kasar a yankin kudancin birnin Managua fadar mulkin kasar.
A karkashin sabuwar dokar yaki da ta'addanci a kasar Nicaragua duk mutumin da aka kama da laifin gudanar da zanga-zangar nuna kin jinin gwamnati ko goyon bayan 'yan adawar kasar, to zai iya fuskantar zaman gidan kurkuku har na tsawon shekaru 20.