Trump:Ganawata Da Shugaba Rouhani Ya Danganta Da Kasar Iran
A Ci gaba da da'awa maras tushe kan kasar Iran, Shugaban kasar Amurka Donal Trump ya ce ganawarsa da Shugaba Rouhani ta ta'alaka da matakin da kasar Iran ta dauka.
Cikin wani rahoto da ya watsa a safiyar yau lahadi, kamfanin dillancin labaran Irna ya nakalto kalamar shugaban Amurka Donal Trump ya watsa a shafinsa na Twitter na riyar cewa Tattalin arzikin kasar Iran ya samu koma baya sosai kuma ko wata rana al'umura na kara tabarbarewa a kasar, kuma ganawata da Shugaban Iran za ta tabbata ko akasin haka, ba shi ke da mahimanci ba, ya danganta da kudirin da kasar ta dauka.
A ranar Litinin din da ta gabata ma Shugaban kasar Amurka Donal Trump ya yi da'awar cewa a shirye yake ya tattauna da shugaban kasar Iran ba tare da gindaya sharadi ba.
Wannan yaudara na Shugaban Amurka musaman ma na bayyana shirinsa na tattaunawa da Shugaban Iran na zuwa ne, bayan ficewar Amurka daga yarjejjeniyar nukiliya da kasar Iran din ta cimma tare da kasashen Duniya tare kuma da bayyana dawo da takunkumin da Amurka ta kakabawa kasar Iran din a baya cikin watani uku zuwa shida.
Wannan mataki da Trump ya dauka ya fuskanci suka daga ciki da Duniya baki daya.