Britaniya Ta Yanke Kauna Kan Yerjejeniyar Ficewa Daga Tarayyar Turai
Ministan kasuwanci na kasar Britaniya ya bada sanarwan cewa rashin tabbas da samun yerjejeniyar ficewar kasar daga tarayyar turai ya kai kashi 60% a halin yanzu.
Liam Fox ya bayyana haka ne a hirar da ta hada shi da jaridar Sunday Times na kasar ta Britaniya a birnin London ya kuma kara da cewa matsalar cimma yerjejeniya da tarayyar Turai ta na da nasaba da rashin cikekken iko da majalisar dokokin tarayyar bata da shi a kan lamarin.
Fox ya ce idan tarayyar turai bata gaggauta cimma yerjejeniya da kasar Britaniya ba to kuwa ta dakaci matsalolin tattalin arziki masu yawa nan gaba.
A wani bangaren kuma jaridar Guardian ta kasar Britania ta bayyana cewa bukatar karin lokaci na tattaunawa kafin a cimma yerjejeniyar ya kara tabbatar da tsoron da ake na cewa Britania ba zata cimma yerjejeniya da tarayyar Turai kafin wa'adin da aka ajiye na watan Maris shekara mai zuwa ba.