Yunkurin Amurka Na Karan Kanta A Kan Kasar Rasha
Shugaban kwamitin harakokin kasa da kasa na Rasha ya sanar da cewa bukatar sanatocin Amurka na bayyana Rasha a matsayin kasa mai goyon bayan 'yan ta'adda, yunkuri ne na nuna kai.
Kamfanin dillancin labaran kasar Rasha Tass ya nakalto Shugaban kwamitin dake kula da harakokin kasa da kasa na kasar Leonid Slutsky na cewa siyasar Washington a yankin gabas ta tsakiya ita ta yi sanadiyar samar da kungiyoyin 'yan ta'adda kamar AlQa'ida, ISIS da jabhatu-Nusra.
Jaridar "Kommersant" ta sanar a jiya laraba cewa na samu wata takarda da wasu sanatocin jam'iyar Republican suka bukaci a kakabawa kasar Rasha sabin takunkumi.
Jaridar ta bayyana cewa Shugaba Trump da kansa ne ya bukaci sanatoci su gabatar da wannan kuduri domin samar da hadin kan kasashen Turai wajen zartar da wannan takunkumi.
Rufe asusun kudaden dala na bankunan Rasha da na shugaba Viladimin Putin a Duniya da kuma amincewa da kasar Rasha a matsayin kasa dake goyon bayan 'yan ta'adda na daga cikin ababen da wannan sabon kudiri ya kumsa.