Akalla Mutum 35 Suka Hallaka Sanadiyar rubtawar Gada A Kasar Italiya
https://parstoday.ir/ha/news/world-i32765-akalla_mutum_35_suka_hallaka_sanadiyar_rubtawar_gada_a_kasar_italiya
Babbar gadar motoci da ta rufta a kusa da birnin Genoa na Italiya ta yi sanadiyar mutuwar akalla mutane sama da 35, abin da ya yi sanadiyar faduwar kanana da manyan motoci daga saman gadar.
(last modified 2019-08-10T10:24:46+00:00 )
Aug 15, 2018 02:03 UTC
  • Akalla Mutum 35 Suka Hallaka Sanadiyar rubtawar Gada A Kasar Italiya

Babbar gadar motoci da ta rufta a kusa da birnin Genoa na Italiya ta yi sanadiyar mutuwar akalla mutane sama da 35, abin da ya yi sanadiyar faduwar kanana da manyan motoci daga saman gadar.

Ministan Sufuri na kasar Italiya, Danilo Toninelli ya bayyana fargabar samun gagarumin ibtila’i sakamakon ruftawar gadar, yayin da jami’an ‘yan sanda ke cewa, kawo yanzu akalla mutane 30 sun rasa rayukansu.

Wata majiyar kasar Italiyan ta sanar da cewa rubtawar gadar ya yi sanadiyar mutuwar mutum 35,da kuma jikkata wasu 13 na daban

Jami’an ‘yan sandan sun alakanta aukuwar lamarin da barkewar iskar hadari mai karfin gaske.

Tuni dai Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya aike da sakon jajantawa zuwa hukumomin Italiya da cewa,Faransa zata aike da ma'aikantan agaji zuwa kasar Italiya.

Shugaban gwamnatin Italiya Giuseppe Conte ya bayyana cewa zai ziyarci wurin da hatsarin ya auku a Genes dake arewacin kasar.