An Cabke Wasu Manyan Jami'an Soja Biyu A Venezuela
Babban lauyan gwamnatin Venezuela Tarek William Saab ta sanar a jiya Talata cewa an cabke wasu manyan jami'an tsaron kasar dake da hannu a yunkurin hallaka Shugaba Maduro.
Kamfanin dillancin Fars ya habarta cewa ya zuwa yanzu hukumomin kasar Venezuela sun kame mutum 14 da ake zargin su da hanu a yunkurin hallaka shugaban kasar Nicolás Maduro.
A ranar lahadi 6 ga watan Agusta ne wani abu ya fashe a lokacinda shugaban kasar ta Venezuela yake jawabi a wani taro da sojojin kasar a birnin Caracas babban birnin kasar.
An dai yi amfani da jirgi maras matuki ne da yake dauke da wasu abubuwa masu fashewa wajen kai harin a loacin da shugaba Maduro yake gabatar da jawabi, lamarin da ya yi sanadiyyar jikkatar sojoji 7.
Gwamnatin Venezuela ta zargi gwamnatocin Amurka da Colombia da hannu wajen shirya yi wa shugaba Maduro kisan gilla, wanda bai yi nasara ba.