Mutane Biliyan Biyu Ne Ke Rayuwa Cikin Talauci A Duniya
https://parstoday.ir/ha/news/world-i32829-mutane_biliyan_biyu_ne_ke_rayuwa_cikin_talauci_a_duniya
A Cikin wani sakamakon bincike da hukumar Human Global Assistance ta fitar na nuni da cewa sama da mutane biliyan biyu ke rayuwa cikin talauci a Duniya
(last modified 2018-08-22T07:02:16+00:00 )
Aug 19, 2018 07:59 UTC
  • Mutane Biliyan Biyu Ne Ke Rayuwa Cikin Talauci A Duniya

A Cikin wani sakamakon bincike da hukumar Human Global Assistance ta fitar na nuni da cewa sama da mutane biliyan biyu ke rayuwa cikin talauci a Duniya

Kamfanin dillancin labaran Anatolio ya habarta cewa cikin wani sabon rahoto da hukumar Human Global Assistance ta 2018 ta fitar na nuni da cewa sama da mutane biliyan biyu ne ke rayuwa cikin talauci a Duniya, sannan kuma akwai wasu miliyan 533 dake rayuwa cikin bakin tatauci ta yadda sai sun fita su samo abincin da za su ci da bakunansu.

Ko wata ranar 19 ga watan Augusta, hukumar ta Human Global Assistance na bayar da rahoto kan matsalolin da mutane suka fuskanta cikin shekara kama daga karamcin ruwa, fari, rikice-rikece da kuma bala'in da al'umma suka fuskanta.

Rahoton ya ce a shekarar bana akalla mutum miliyan 201 ke bukatar taimakon gaggawa domin su ci gaba da rayuwa a kasashe 134 na Duniya, a kasar Yemen kadai akwai mutun miliyan 20 dake bukatar taimakon gaggauwa kamar yadda a kasar siriya akwai miliyan 14.