Trump Ya Dakatar Da Ziyarar Pompeo Zuwa Korea Ta Arewa
https://parstoday.ir/ha/news/world-i32900-trump_ya_dakatar_da_ziyarar_pompeo_zuwa_korea_ta_arewa
A jiya juma'a shugaban kasar Amurka Donal Trump ya dakatar da ziriyar Saktaren harakokin wajen kasar Mike Pompeo zuwa kasar Korea ta Arewa bisa da'awar rashin ci gaba na kakkabe makaman nukiya a tsibirin Korea.
(last modified 2018-08-25T00:54:26+00:00 )
Aug 25, 2018 00:54 UTC
  • Trump Ya Dakatar Da Ziyarar Pompeo Zuwa Korea Ta Arewa

A jiya juma'a shugaban kasar Amurka Donal Trump ya dakatar da ziriyar Saktaren harakokin wajen kasar Mike Pompeo zuwa kasar Korea ta Arewa bisa da'awar rashin ci gaba na kakkabe makaman nukiya a tsibirin Korea.

Cikin wani sako da ya rubuta a shafinta na Twitter, Shugaban kasar Amurka Donal Trump ya ce mun bukaci Mike Pompeo da ya dakatar da ziyarar da zai kai kasar Korea ta Arewa domin a ganinsa babu wani ci gaba da aka samu kan batun rusa cibiyoyin nukiliyar kasar.

Har ila yau Shugaba Trump ya bayyana dakatar da ziyarar Pompeo da ya yi zuwa gabashin Asiya  bisa riyar yakin kasuwanci da kasar Sin inda ya ce har yanzu ya kasa yardar cewa mahukuntan Pekan na taimakawa wajen rusa makaman nukiya a tsibirin Korea kamar yadda suke a baya.

A cikin wannan mko ne aka sa ran sakataren harakokin wajen Amurkan Panpeo zai kai ziyara kasar Korea ta arewa a karo na hudu.

Wannan firici na Trump na zuwa a yayin da kasar Korea ta arewa ta rusa wasu cibiyoyinta na Nukiliya, a makunin da suka gabata, da nufin tabbatar da sulhu a yankin, to saidai ya zuwa yanzu babu wani abu da mahukunta Washington suka yi a game da yarjejjeniyar birnin Singapore.