Shugaba Trump Ya Goyi Bayan Kafa Kasar Palasdinu
A karon farko shugaba Trump na Amurka ya goyi bayan samar da kasar Falasdinu domin kawo karshen takaddamar da ake tsakanin Palastinawa da yahudawa
A cikin wani jawabi da ya gabatar a wannan alhamis shugaba Donal Trump na Amurka ya bayyana goyon bayansa na samar da kasar Palastinu da kuma haramtacciyar kasar Isra'ila ta yadda za a kawo karshen takadama tsakanin Palastinawan da aka mamaye musu kasarsu da kuma 'yan sahayuna.
Tsarin Majalisar Dinkin Duniya na shekarar 1947 ya tanadi bai wa Isra'ila da Palasdinu ‘yancin cin gashin kai kowacce, yayin da birnin Kudus ya kasance karkashin wata hukuma daban ta kasa da kasa, sai dai shugabannin Larabawa sun ki amincewa da tsarin.
Daga bisani ne aka gabatar da yarjejeniyar Oslo ta shekarar 1990 da ake ganin za ta bai wa Isra'lan da Palasdinawa ‘yancin cin gashin kai, amma wannan yarjejeniya ba ta je kai koina ba.
Yanzu haka jagoran Palasdinawa, Mahmud Abba na ci gaba da neman ganin an aiwatar da yarjejeniyar shekarar 1967 da za ta bai wa Yahudawan Isra'ila kasarsu daban, su ma Palasdinawa tasu daban.
Shi kuwa Firaminstan H K Isra'ila Benjamin Netanyahu na cewa, karkashin dukkan wata yarjejeniya dole ne Isra'ila ta karbi harakoki tsaro na yankin.