Canada Ta Kwace Takardar Zama 'Yar Kasarta Ga Shugabar Myanmar
(last modified Fri, 28 Sep 2018 17:30:03 GMT )
Sep 28, 2018 17:30 UTC
  • Canada Ta Kwace Takardar Zama 'Yar Kasarta Ga Shugabar Myanmar

Gwamnatin Canada, ta amince da bukatar kwace takardar zama dan kasa ga shugabar kasar Myanmar, Aung San Suu Kyi, saboda yadda tayi gum da bakinta akan kisan kiyashin 'yan Rohongyas.

Majalisar dokokon Canada ce ta kada kuri'ar bukatar hakan da gagarimin rinjaye, a yayin da gwamnatin kasar ta aiwatar da hakan, duba da yadda shugabar kasar ta Myanmar ta ki cewa uffan kan batun kisan kiyashin Musulmin na Rohingyas.

A shekara 2007 ne majalisar dokokin Canada ta baiwa Aung San Suu Kyi, dake da lambar yabo ta zaman lafiya, takardar zama 'yar kasarta a lokacin da ake tsare da ita a kurkuku.

Mutuncin, Aung San Suu Kyi dai ya zube ne a idon duniya, saboda kin yin allawadai da kuma tsawatawa sojojin kasarta dasu dakatar da cin zarafi da walakancin da suke wa 'yan kabilar ta Rohiongyas, wanda MDD ta danganta da yunkurin share wata kabila daga doron kasa.

A tsakanin watan Agusta zuwa Disamba na 2017, sama da musulmin Rohingyas 700,000 ne suka tsare daga muhallansu zuwa makobciyar kasar Bangaladesh, domin kaucewa cin zarafi, fyade, kisa, daga sojojin Myanmar.