MDD:Yaki Ya Raba Yamaniyawa Kimanin Miliyan 8 Da Aikinsu
https://parstoday.ir/ha/news/world-i33403-mdd_yaki_ya_raba_yamaniyawa_kimanin_miliyan_8_da_aikinsu
Hukumar bunkasa ci gaban kasashe ta MDD ta sanar da cewa kimanin yamaniyawa miliyan 8 ne suka rasa aikinsu sanadiyar yaki.
(last modified 2018-09-30T02:59:06+00:00 )
Sep 30, 2018 02:59 UTC
  • MDD:Yaki Ya Raba Yamaniyawa Kimanin Miliyan 8 Da Aikinsu

Hukumar bunkasa ci gaban kasashe ta MDD ta sanar da cewa kimanin yamaniyawa miliyan 8 ne suka rasa aikinsu sanadiyar yaki.

A cikin wata sanarwa da ta wallafa a shafinta na Twutter, hukumar bunkasa ci gaban kasashe ta Majalisar Dinkin Duniya yakin da aka kallafawa kasar yemen ya yi sanadiyar raba kimanin mutune milyan 8 da ayyukansu, wanda hakan kuma ya sants sama da 'yan kasar miliyan 22 ke bukatar taimakon gaggauwa.

A rahoton da ta fitar na baya-bayan nan hukumar abinci ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce a halin da ake cikin kasar Yemen na cikin tsananin mawuyacin hali na matsalar rashin abinci a Duniya , a ko wata ta Allah, yunwa na kashe mutane da dama a kasar.

Tun a watan Maris din 2015 ne kasar Saudiya da hadaddiyar daular Larabawa bisa cikekken goyon bayan Amurka da wasu kasashen yankin suka fara kai hare-haren wauce gona da irin kan al'ummar kasar Yemen tare da killace kasar ta sama da ruwa da kasa.kuma ya zuwa yanzu yakin ya salwanta rayukan mutum sama da dubu 14 tare da jikkata wasu dubai na daban da kuma raba wasu milyoyin da mahalinsu.