Sharhi: Rashin Nasarar Ziyarar Yarima Mai Jiran Gadon Saudiyya Zuwa Kuwait
Kafafen watsa labarai sun ba da rahoton cewa ziyarar da yarima mai jiran gado na Saudiyya, Yarima Muhammad bn Salman ya kai Kuwait don neman goyon bayan sarkin kasar, ta zamanto wata ziyara maras sakamako.
A ranar lahadin da ta gabata ce dai Yarima Muhammad bn Salman din ya kai wannan ziyarar zuwa kasar Kuwait, wacce saboda rashin cimma manufar da aka yi ta ba ta dau sama da sa'oi hudu ba inda Yariman ya dawo Riyadh hannun rabbana. Masana dai suna ganin babban dalilin rashin nasarar wannan ziyara shi ne irin yanayin Yariman da kuma bukatar da ya gabatar wa sarkin Kuwaitin.
Masana halayen dan'adam dai suna bayyana Bn Salman a matsayin wani mutum mai fuskoki biyu. Wato mutum ne wanda ya kasance mai mika kai da kaskantar da kanta a gaban gwamnati da kuma jami'an Amurka, to amma a gaban kasashen larabawan Tekun Fasha kuma yana nuna musu girman kai da nuna isa. Hakan shi ne dalilin da ya haifar da irin rikicin da ya kunno kai tsakanin Saudiyya din da kasar Qatar tsawon watanni 15 din da suka gabata. Kafafen watsa labarai sun ce Yarima Muhammad din da irin wannan kallo da yanayi na girman kai ya tafi kasar Kuwait, to sai dai ya fuskanci mayar da martani da kin amincewar sarkin Kuwait, wanda ya sanar da Bn Salman din cewa kasarsa ba za ta amince da irin wannan mu'amala ta sa ta girman kai da nuna isa ba.
Batu na biyu kuma yana da alaka ne da bukatar da Bn Salman din ya gabatar wa jami'an kasar Kuwait. A fili yake cewa akwai sabani tsakanin Kuwait da Saudiyya musamman kan batun man fetur. Don haka a yayin wannan ziyarar yariman Saudiyyan ya so ne a magance wannan sabanin, to sai dai ya nuna son kai don kuwa yana son komai ya zamanto ta hanyar da zai amfani Saudiyya din ne ba tare da la'akari da muradan kasar Kuwait din ba. Rahotanni sun ce Bn Salman din cikin girman kai da isa ya bukaci Kuwait da ta mika wa Saudiyya wani yanki da ake bangaren Kuwait din ga Saudiyya ko kuma ta biya tarar Dinare biliyan 20 ga Saudiyyan, lamarin da kasar Kuwait din ta ki amincewa da shi, inda Sarki ya ba da umurnin a kawo karshen wannan tattaunawar sannan kuma nan take Yarima Muhammad Salman ya bar kasar.
Wani abu kuma da ake ganin ya fusata jami'an Kuwait din shi ne kokarin da Bn Salman din yayi na gabatar da wata bukata ta shugaban Amurka Donald Trump ta kara irin man fetur din da kasar Kuwait din take tonowa da kuma sayar da shi a kasuwar duniya, lamarin da kasar Kuwait din ta ki amincewa da shi.
Ko shakka babu wannan ziyarar maras sakamako tana daga cikin shan kashi mai muhimmanci da Bn Salman din ya fuskanta tsawon lokacin da ya dafe madafan iko a Saudiyya don kuwa hatta a yayin barinsa kasar Kuwait din yarima mai jiran gadon kasar ta Kuwait ya ki ya raka shi filin jirgin, sai dai ministan harkokin wajen kasar ne yayi masa rakiya.