Amurka : Hillary Clinton Ta Soki Siyasar Trump
Clinton wacce tashar talabijin din CNN ta yi hira da ita ta ce salon mulkin Trump ya raunana aiki da doka a cikin kasar
Hillary Clinton ta kuma zargi shugaban na Amurka da ba da dama ga batun cin hanci da rashawa ya watsu a cikin kasar da kuma a tsakanin na kusa da shi da su ka hada da iyalansa.
Tsohuwar ministar harkokin wajen ta kasar Amurka ta ci gaba da cewa; Ahalin da ake ciki a yanzu, al'ummar kasar sun dawo daga rakiyar cibiyoyi da dama na kasar da su ka hada da coci-coci da kuma majalisar dokoki
Hillary Clinto ta zargi Trump da halayyar danniya saboda yadda yake jinjinawa 'yan kama karya.
Saboda karatowar zabuka a Kasar ta Amurka, manyan jam'iyyun biyu na kasar sun bude sukar junansu da tuhumarsu da rashin siyasa mai inganci.